Wednesday, June 18, 2008

FALALAR AIKIN HAJJI

FALALAR AIKIN HAJJI

Allah ya kwadaitar damu yin aikin hajji kuma ya bayyana d'umbin ladar da za'a samu a sakamakon hakan hadisan dasuke zuwa zasu bayyana haka:

Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam : ( Duk wanda yayi Hajji, be yi rafasu ba - wato beyi Jima'i a cikinsa ba- kuma beyi fasikanci ba –wato sab'on Allah- ze koma mara laifi kamar randa mahaifiyarsa ta haifeshi ) Bukhari da Muslim.

Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam : (Yin aikin Umurah zuwa Umurah ana kankare zunubbai dake tsakaninsu, shiko aikin Hajji karbabbe baya da sakamako se Aljanna.) Bukhari da muslim.

Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam : yayinda aka tambayeshi gameda mafificin ayyuka se yace " Imani da Allah da manzansa" akace seme kuma? Yace "se jihadi dan daukaka kalmar Allah" akace se me kuma? Yace" se aikin Hajji karbabbe". Bukhari da Muslim.

Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam………………..

SHARUDDAN WAJABCIN HAJJI

Seda sharudda masu zuwa hajji yake zama wajibi:

1. Musulunci

2. Balaga

3. Hankali: wato yakasance me hankali domin Hajji baya wajaba akan mahaukaci.

4. Y'anci: wato yazama d'a,domin hajji baya zama wajibi akan bawa. Dalilan wadannan sun gabata a cikin rukunin Azumi.

5. Samun iko: kamar yadda Allah madaukakin Sarki yace ( kuma lallai Allah ya wajabta wa mutane yin Hajjin dakinsa ga wanda yasami iko….) Sur. al'imrana -97.

HUKUNCIN AIKIN HAJJI

Yin aikinHajji wajibine akan kowani musulmi na miji da musulma mace dasuke da iko. Kuma aikin Hajji ya tabbata acikin Littafi da Hadisi da Ijma'i.

Daga cikin Littafi : Allah madaukakin Sarki Yace: ( kuma lallai Allah ya wajabta wa mutane yin Hajjin dakinsa ga wanda yasami iko,kuma duk wanda ya kafirce to lallai Allah mawadaci ne ga Halittu.) Sur. Al'imrana

Daga Hadisi : Abdullahi dan Umar ya ruwaito Hadisi daga Mnazan ALLAH Sallalllahu Alaihi Wasallam yace: ( An gina musulunci ne akan abubuwa guda biyar : Shaidawa babu abin bautawa da can canta se Allah kuma Annabi Muhammadu Manzan Allah ne,Tsayar da Sllah, Bayar da Zakkah, Yin Hajji da kuma Azumin Watan Ramadana) Bukhari da muslim.

Daga Ijmaa'I : Dukkan Musulmai sun hadu akan wajabcinshi kuma dayane daga cikin rukunnan musulunci, kuma abune da kowa yasanshi acikin Addini, kuma duk wanda yyi musunsa to ya kafirta kuma yaayi rudda daga musulunci, haka kuma malamai sun hadu akan cewa aikin Hajji baya wajaba face sau d'aya a rayuwar mutum se dai idan mutum musulmi yayi bakancensa wato alwashi to yazama dole ya cika alwashinsa, amma duk abinda yayi bayan wannan to neman lada ne kawai.

Abdullhi dan Abbabs Allah yakara yarda agareshi yace Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yayi mana Khud'uba, se yace: (Yaku mautane Allah ya wajabta aikin Hajji akanku ) se Ak'ra'a bin Habis yace "Shin kowace shekarane ya manzan Allah? Se yayi shiru har se da ya maiamaita hakan sau Uku, sannan Manzan Allah Sallallahu Alaihin Wasalllam yace : ( da'ace nace E da yazama wajibi, kuma da dayazama wajibi bazaku yiba kuma bazku iyaba, Hajji sau dayane duk wanda yakara to neman ladane ) Ahmad, Abu dawud da Nasa'i.

Ma'anar Hajji

Menene Ma'anar Hajji?
Hajji a harshen larabci ma'anarsa itace nufi ko aiki da yake zuwa lokaci zuwa lokaci,
Amma a musulunci, idan akace hajji shine Nufin dakin Allah me alfarma domin aiwatar da wasu ayyuka kebantattu da Alalh madaukakin sarki ya ambata acikin littafinsa kuma Hadisai sukayi bayani akansu.